News
Gwamnatin Tarayya Ta Mallakawa Kanta Bankin Keystone Bayan Hukuncin Kotu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Tarayya ta karbe ragamar gudanarwar bankin keystone daga karkashinsa sakamakon wani hukuncin da koto ta yanke a jihar Legas.
Cikin Hukuncin da mai shari’a, Rahman Oshodi ya yanke ya ce hukuncin ya biyo bayan dokar da Bankin Keystone ya karya na rashin isasshen kudaden hannun Jari Naira Billion 6.3 na dokokin Gwamnatin Tarayya.
Hukuncin da kotun ta yanke a ranar 11 ga Fabrairu , 2025 kotu ta bada umarnin karbe bankin har sai lokacin da Bankin ya cike dukkanin ka’doji.
Haka zalika kotun ta ce muddin Bankin ya gaza cike dukkanin kaidoji za ta cigaba da gudanar dashi tare da baiwa gwamnatin Tarayya damar sabuntashi rijista zuwa mallakinta.
Tun a ranar 10 ga Janairu, 2024, Babban bankin Najeriya CBN ya ba da sanarwar rushewar kwamitin bankin sabida rashin cike ka’doji “wanda yasa EFCC ta hannun gwamnatin ta shigar dashi Kara.
Sai dai duk da rikicin, bankin ya ce yana tabbatarwa da abokan mu’amalasa cewa komai zai dawo dai dai Kuma zai cike dukkanin wasu sharadai.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
