Connect with us

News

Tarihi: Kisan Gilla da Aka Yi wa Janar Murtala Muhammed a Rana Irin Ta Yau

Published

on

FB IMG 1739446523100

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

A rana irin ta yau, 13 ga Fabrairu, 1976, Najeriya ta tsinci kanta cikin rudani bayan wasu sojoji maciya amanar kasa, karkashin jagorancin Lftanal Kanal Buka Suwa Dimka, suka kashe shugaban mulkin sojin Najeriya, marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed.

An kai harin ne a birnin Lagos yayin da shugaban ke kan hanyarsa ta zuwa ofis. Wannan kisan gilla ya girgiza Najeriya, domin Murtala Muhammed ya shahara a matsayin shugaba mai kishin kasa, wanda ya yi kokarin kawo sauyi cikin mulki da tattalin arzikin kasar.

Mutuwarsa ta haifar da gagarumin martani daga hukumomin tsaro, wanda ya kai ga dakile yunkurin juyin mulkin da kuma cafke wadanda suka shirya wannan aika-aika. Daga bisani, Mataimakinsa, Janar Olusegun Obasanjo, ya karbi ragamar mulkin kasar.

An haife shi a Kano, 8 Nuwamba 1938 ya fara aikin sojin Nijeriya ne bayan kammala Makarantar sojin Royal Military Academy, Sandhurst. Ya zama Birgediya Janar a shekarar 1971, yana da shekaru 33, ya zama daya daga cikin manyan hafsoshin sojan Nijeriya.

Kisan Murtala Muhammed ya kasance daya daga cikin manyan al’amuran da suka yi tasiri a tarihin Najeriya, kuma har yau ana tuna irin rawar da ya taka a kokarin gina kasa mai adalci da ci gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending