News
Mata 1,511 Sunyi Nasarar Zama Jami’an Hukumar Yan Sanda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar Yan Sanda ta Ƙasa (NPF) ta ce Mata 1,511, ne sukayi nasarar samun horo domin zama Jami’anta na dindin din a jihar Akwa Ibom .
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Baba Azare, ya ce jami’an sunyi nasarar samun ne bayan horan da suka samu na tsawan watanni Uku a wajen Yan Sanda ta Ƙasa.
Mista Azare ya ce an baza jami’an dukkanin sassan Jihar domin magance matsalolin tsaron gidajen Al’umma da ta addabi yankin.
Ya ce wannan horo ba kawai motsa jiki bane na yau da kullun; Wani yunƙuri ne na dabarun yadda Jami’anmu mata zasu yi aiki tuƙuru domin cetan kasarsu.
Haka zalika Mr, Azare ya yaba da sadaukar da Jami’anta mata suka bayar tare da jinjinawa babban sufeto na Yan Sanda, IG Kayede Egbetokun, .
Advertisements
