Connect with us

News

Ƴan’sanda Sun Kama Saurayin Da Ya Kashe Budurwarsa Dan Yi’Yi Tsafi Da Ita A Facebook 

Published

on

1739724486207

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Rundunar Ƴansandan jihar Kwara sun yi nasarar kama wani saurayi, mai suna  Abdulrahman Bello, wanda ake zargi da Kashe budurwarsa Hafsoh Lawal, dalibar da ke shirin kammala karatu a kwalejin Ilimi ta Kwara State College of Education.

Mai magana da yawun ‘yansanda, Toun Ejire-Adeyemi, ne ya tabbatar da kama Abdulrahman Bello mai shekaru 25 a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Advertisement

‘Yansanda sun bayyana cewa an fara neman Hafsoh ne bayan mahaifinta Ibrahim A. Lawal ya kai rahoto cewa ta fita halartar bikin suna a ranar 10 ga Fabrairu, 2025, amma ba ta dawo gida ba. Duk ƙoƙarin kiran wayarta ya ci tura.

 

Advertisement

Bayan bincike ta hanyar fasaha, an gano inda wayarta take, tare da samun gawarta da saurayin ya daddatsa a cikin Durom wanda hakan ya kai ga kama Abdulrahman Bello. Lokacin da aka kama shi, ya amince da laifin kisan Hafsoh da nufin yin sihirin kudi na (oshole/ajoo owo).

 

Advertisement

Rahotanni sun tabbatar da Hafsa sun hadu da saurayita Abdurrahman ne a kafar sada zumunta ta Facebook wacce suka fara soyayya

Tuni dai aka tura Abdulrahman zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) Ilorin, domin zurfafa bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.

Advertisement

Shima mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana takaici kan wannan ɗanyen aiki, yana mai cewa “abin baƙin ciki ne, kuma yana da ban tsoro sannan ya bukaci malaman Juma’a dasu Kara dage tsange wajen yiwa Jama’a nasiha.

Ya buƙaci iyaye su ƙara sa ido kan ‘ya’yansu, tare da kula da irin mutanen da suke mu’amala da su.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending