Connect with us

News

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Ragu Zuwa Kashi 24.48 —Hukumar NBS

Published

on

FB IMG 1739888126429

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 24.28% a watan Janairu daga 28.80% a watan Disamba 2024.

Babban jami’in kididdiga na tarayya kuma shugaban hukumar NBS, Adeyemi Adeniran, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin kaddamar da rahoton sake fasalin farashin kayayyakin masarufi (CPI) a ranar Talata.

Duk da Kashe Sama da Tiriliyan 7 a Lantarki, Ƴan Najeriya na Ci gaba da Fama da Matsalar Wuta

A halin yanzu, ‘yan Najeriya sun fara jin sauƙi, musamman a fannin kayayyakin abinci, inda farashi ke ci gaba da yin ƙasa a kasuwanni da dama. Wasu dillalai sun bayyana cewa saukar farashin kayan abinci yana ƙaruwa kowacce rana, lamarin da ke ƙara shafar manoma da ‘yan kasuwa.

 

Wani ɗan kasuwa da PREMIUM TIMES ta zanta da shi ya ce akwai yiwuwar farashin zai ci gaba da faɗuwa, kasancewar kayan abinci na ƙara samuwa a faɗin ƙasar.

Advertisement

Ba kayan abinci kawai ba, har da sauran kayan masarufi, ana ci gaba da samun raguwar farashinsu, lamarin da ke ba masu saye da ‘yan kasuwa sabbin fata na samun sauƙia kasuwa.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending