Connect with us

News

RAMADAN: Kada Ku Yi Amfani da Gurbatattun Kaya Wajen Bada Sadaka  – Babban Limamin Jami’a

Published

on

sadaka

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Babban Limamin Jami’ar Jihar Legas, Farfesa Amidu Sanni, ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da da’a, kyautatawa, da bayar da agaji yayin da aka fara azumin watan Ramadan.

Advertisement

Sanni ya bayyana cewa bayar da sadaka da kyautatawa ga mabukata su ne alamomin watan Ramadan, don haka yana da muhimmanci a bayar da kyauta mai kyau ba wai gurbatattun kaya ba.

Gwamnatin Tarayya Ta Zargi Shugabannin Ƙananan Hukumomi da Ƙin Buɗe Asusun Banki A CBN

Malamin ya bayyana hakan ne a wata zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Legas ranar Asabar, inda ya taya al’ummar Musulmi murnar shigowar watan Ramadan.

Advertisement

Ya ce Ramadan lokaci ne na tsarkake ruhi da kusanci da Allah, ba wai kawai kamewa daga abinci, sha da mu’amalar jima’i daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending