News
Kuskure Ne Fara Cin Abinci Tun Daga Gida Kafin Fara Tafiya Ga Mai Ajiye Azumin Ramadan – Sheikh Pantami
DAGA YAISR SANI ABDULLAHI
Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa ba ya halatta mai azumi ya fara cin abinci tun daga gida kafin fara tafiya a watan Ramadan.
Malamin ya bayyana hakan ne yayin tafsirin Alƙur’ani da yake gudanarwa, inda ya bayyana cewa izinin ajiye azumi a halin tafiya yana farawa ne kawai bayan an fara tafiya.
Ƴan Ta’adda Sun Kashe Yan Bijilanti 12 Da Yin Garkuwa Da 4 A Zamfara
Ya ce:”Idan mutum yana da niyyar tafiya, ba shi da damar ajiye azumi har sai ya kama hanyar tafiya. Amma idan yana gida, dole ne ya ci gaba da azumi har sai ya fara tafiya.”
Sheikh Pantami ya yi kira ga al’umma da su kiyaye wannan doka, domin kauce wa kuskuren da yawa ke tafkawa a lokacin Ramadan.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
