Connect with us

News

Hukumar Hisba Ta Kulle Shagon Caca A Cikin Watan Ramadan A Kano 

Published

on

Hukumar Hisbah Haramta Zancen Dare A Mota A Kano

DGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kulle wani shagon caca da ke cikin birnin Kano, sakamakon karya dokar jihar da kuma saba wa al’adar musulunci a cikin watan Ramadan.

Advertisement

Muƙaddashin babban kwamandan Hisba  Sheikh Mujahiddin Aminuddin, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙon murya da ya aiko wa jaridar Indaranka, inda ya bayyana cewa matakin ya dace da tanadin dokokin jihar Kano na hana duk wata harkar da ta sabawa koyarwar addini, musamman a cikin watan azumi.

Sabon Rikici Ya Sake Barkewa Tsakanin Jiga Jigan Siyasar NNPP Kwankwasiyya a Kano

Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda wasu musulmi ke halartar irin waɗannan wurare domin yin caca duk da kasancewar watan Ramadan, wanda ya kamata a ƙara kusanci da Allah.

Advertisement

Hukumar Hisba ta ja kunnen al’umma da su guji aikata abubuwan da ka iya karya doka ko sabawa addini, tare da yin kira ga masu irin waɗannan shaguna da su dakatar da sana’ar da ba ta dace ba a jihar Kano.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending