News
Hukumar Shari’ah Ta Jihar Kano Ta Kaddamar Da Sabbin Kwamitoci Don Inganta Shari’a
Hukumar Shari’ah ta Jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta, Sheikh Malam Ali Dan Abba, ta kaddamar da sabbin kwamitoci domin kawo sauye-sauye masu ma’ana wajen cigaban shari’a a jihar.
Taron kaddamarwar ya samu halartar manyan baki da suka hada da tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Kano (Ungoggo Branch), Barr Mujiburrahman, mai magana da yawun kotuna ta jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, wakilin shugaban gidajen gyaran hali, wakilin kwamishinan ‘yan sanda SP Abdullahi Haruna Kiyawa, manyan malamai, da mambobin hukumar.
Mutum 1,010 Sun Mutu Sakamakon Hare-hare A Watan Fabrairu – Rahoto
Sheikh Malam Ali Dan Abba ya bayyana cewa babban burin kafa wadannan kwamitoci shi ne karfafa sulhu da inganta tarbiyya a tsakanin al’umma, tare da hana shaye-shaye, kwacen waya, da tabarbarewar zamantakewa.
Ya jaddada cewa tsaida sallah na da muhimmanci wajen magance wadannan matsaloli, yana mai fadin cewa hukuma za ta mayar da hankali kan ilimantar da al’umma da karfafa hadin kai tsakanin limamai da ladanai.
Kwamitocin da aka kafa sun hada da:
Kwamitin Sulhu, Kwamitin Da’awa ,Kwamitin Tantance Limamai da Ladanai ,Kwamitin Bita da Wayar da Kan Al’umma Kan Addini.
Tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Kano, Barr. Mujiburrahman, ya yaba da kokarin gwamnati, yana mai cewa tun bayan mulkin Malam Ibrahim Shekarau ba a taba samun irin wannan ci gaba ba. Ya bukaci gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya inganta ayyukan hukumar don dorewar shari’a a jihar.
Shima Baba Jibo Ibrahim ya tabbatar da cewa kwamitin sulhu zai taimaka wajen inganta shari’a, inda ya bayyana cewa duk sulhun da aka kulla za a tabbatar da shi ta fuskar doka don gujewa masu kin bin umarni.
Taron ya gudana cikin nasara, inda aka roki Allah da ya ba kwamitocin ikon gudanar da aikinsu yadda ya kamata domin ci gaban jihar Kano da kasa baki daya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
