News
Dalilin Da Ya Sanya Rundunar ‘Yan Sandan Kano Karrama Wakilin Muhasa TV & Radio
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta karrama Mujahid Wada Guringawa, daya daga cikin ma’aikatan tashar Muhasa TV & Radio, bisa kwazo da jajircewarsa wajen bayar da rahotanni da suka shafi tsaro da zaman lafiya a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana haka yayin bikin karrama kwamishinan ‘yan sandan jihar mai barin gado, AIG Salman Dogo Garba, wanda ya samu karin girma zuwa mataimakin babban sufeton ‘yan sanda na kasa.
Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Shirin Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16
Mujahid Wada ya shahara wajen zakulo rahotanni masu inganci kan ayyukan rundunar ‘yan sanda, lamarin da ya taimaka wajen wayar da kan jama’a kan mahimmancin tsaro da zaman lafiya a Kano. Bikin karramawar ya gudana a wajen shakatawar manyan jami’an ‘yan sanda da ke Bompai, Kano.
Rundunar ta yaba da irin rawar da tashar Muhasa TV & Radio ke takawa wajen fadakar da al’umma, tare da yi musu fatan alheri a ci gaba da gudanar da aikinsu. AIG Salman Dogo Garba ne ya mika lambar yabo ga Mujahid Wada a hedkwatar ‘yan sanda da ke unguwar Bompai.
AIG Salman Dogo Garba, bayan karin girman da ya samu, zai koma kula da rundunar ‘yan sanda ta kasa a shiyya ta 5, wadda ta hada da jihohin Edo da Delta.
Da yake nuna farin cikinsa, Mujahid Wada Guringawa ya ce wannan karramawa wata gagarumar dama ce da za ta kara masa kwarin gwiwa wajen gudanar da aikinsa. Ya kuma yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani abu da ba a amince da shi ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Shugaban kwamitin hadin gwiwar ‘yan sanda da jama’a (PCRC) na jihar Kano, Dokta Ali Hassan Tudun Bayero, ya gode wa AIG Salman Dogo bisa namijin kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a Kano.
Abokan aikinsa a Muhasa TV & Radio sun taya Mujahid Wada murna, tare da yi masa fatan alheri a ci gaba da jajircewa wajen aikin jarida.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
