Connect with us

News

Gobara Ta Lakume Rayuka 7, Ta Haddasa Asarar Naira Miliyan 50 A Kano

Published

on

 

Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da gobara ta haddasa asarar kadarori na sama da Naira miliyan 50 a Jihar Kano a watan Fabrairun 2025.

Advertisement

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa hukumar ta samu jimillar kiraye-kirayen kashe gobara guda 77, kiraye-kirayen neman ceto 11, da kuma ƙaryar kiran gobara guda uku a cikin watan.

Dalilin Da Ya Sanya Rundunar ‘Yan Sandan Kano Karrama Wakilin Muhasa TV & Radio

Ya ƙara da cewa, an kiyasta darajar kadarorin da gobarar ta lalata a cikin watan Fabrairu da N50,318,000, yayin da jami’an kashe gobara suka ceto kadarori da darajarsu ta kai N180,318,000.

Advertisement

Hukumar ta yi kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan wajen amfani da wuta domin gujewa afkuwar gobara, tare da shawarci direbobi da su tuka mota cikin kulawa da bin dokokin hanya don guje wa haɗurra.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending