Connect with us

News

Zargin Neman Kujerar Sanatan Kano Ta Kudu: Wani Matashi Ya Yi Wa Shugaban Ma’aikatan Kano Wanki Babban Bargo

Published

on

FB IMG 1742997838467

Wani matashi mai suna Shuaibu Haruna daga yankin Kiru/Bebeji ya aikewa da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano, Alhaji Abdullahi Musa, wata buɗaɗɗiyar wasika mai cike da zafafan tambayoyi da suka shafi yankin Kano ta Kudu.

A cikin wasikar, matashin ya zargi Shugaban Ma’aikatan da rashin amfani da damar da yake da ita wajen inganta yankin da ya fito, duk da kasancewarsa cikin manyan masu yanke hukunci a Jihar Kano. Haruna ya bayyana cewa, a tsawon shekarun da Alhaji Abdullahi Musa ya shafe a gwamnati, bai ga wani gagarumin ci gaba da ya kawo wa yankin ba, duk da matsayinsa mai tasiri.

Ƙudurin Cire Kariya Ga Gwamnoni Da Mataimakansu Ya Tsallake Karatu Na Biyu

A wasikar, matashin ya jaddada cewa, yankin Kiru/Bebeji da Kano ta Kudu gaba ɗaya na fama da matsalolin rashin kyawawan makarantu, asibitoci, hanyoyi da kuma ruwan sha, amma har yanzu ba a ga wani kokari daga Shugaban Ma’aikatan ba wajen magance waɗannan matsaloli.

Haruna ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ake zargin Shugaban Ma’aikatan na hararar wasu daga cikin ‘yan yankin daga samun muƙamai masu tsoka a cikin gwamnati, yana mai cewa hakan na iya zama wani yunkuri na hana su tasiri a siyasa, musamman idan har suna da burin takarar kujera a nan gaba.

Ya ce, “Idan har da gaske Maigirma Shugaban Ma’aikata na da burin zama Sanatan Kano ta Kudu, to yana da kyau ya fara tabbatar da cewa ya taimaka wa jama’arsa kafin su amince da shi a matsayin wakilinsu a matakin ƙasa.”

Wannan wasika ta tayar da ƙura a kafafen sada zumunta, inda da dama ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan cancantar Shugaban Ma’aikatan da rawar da yake takawa a siyasar yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending