News
Hatsarin Mota A Kano: Mutane 2 Sun Rasu, Wasu Sun Jikkata
Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC), reshen jihar Kano, ta tabbatar da afkuwar wani mummunan hatsarin mota da ya lakume rayukan mutane biyu tare da jikkata wasu a titin Airport Road, Kano.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba da misalin karfe 8:15 na safe, inda wata mota kirar DAF ta yi karo da babur kirar Jincheng.
Kakakin hukumar FRSC a Kano, CRC Abdullahi Labaran, ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da mutane shida. Cikin su, biyu sun rasu nan take, yayin da mutum guda ya samu raunuka, sai kuma sauran uku da suka tsira ba tare da munanan raunuka ba.
A cewar Labaran, rashin bin ka’idojin tuki ne ya haddasa hatsarin. Bayan faruwar lamarin, jami’an FRSC sun garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammed domin kula da lafiyarsu, yayin da aka kai gawarwakin marigayin zuwa Asibitin Malam Aminu Kano domin tabbatar da rasuwarsu.
Hukumar ta kuma mika motocin da sauran kayayyakin da aka samu a wurin hatsarin ga ofishin ‘yan sanda na Gwagwarwa domin ci gaba da bincike.
Kwamandan hukumar FRSC na Kano, Umar Mas’udu Matazu, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da yi musu addu’a, sannan ya bukaci masu ababen hawa da su rika bin dokokin hanya domin rage yawan hatsura a tituna.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
