News
Sarki Aminu Ado Bayero Ya Janye Hawan Sallah Ƙarama Saboda Dalilin Tsaro
Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana janye gudanar da Hawan Sallah Ƙarama na wannan shekarar, yana mai bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda dalilin tsaro da halin da Kano ke ciki a halin yanzu.
Sarkin ya sanar da wannan matsaya ne a yayin taron manema labarai da ya gudanar a yau, inda ya yi kira ga al’ummar Kano da su yi hakuri da kuma bin doka da oda a wannan yanayi da aka tsinci kai.
INEC Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Ce Kiranyen Sanata Natasha Yanzu Yana Kan Ka’ida
Wannan mataki ya biyo bayan kokarin samar da kwanciyar hankali da kauce wa duk wani abu da ka iya kawo rudani a fadar masarautar.
Jama’a da dama sun karɓi wannan sanarwa da fatan alheri, tare da addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.
