News
Waɗanda Zakkar Fidda-Kai Ta Wajaba A Kansu Da Muhimmancinta Ga Al’umma
Malamai sun bayyana cewa Zakkar Fidda-Kai ta fara wajabta ta ne bayan hijirar Annabi Muhammad (SAW) da shekaru biyu, a daidai lokacin da aka wajabta azumin Ramadan. Wannan zakka tana da matukar muhimmanci wajen kyautata zamantakewa da tabbatar da jin dadin al’umma.
Waɗanda Zakkar Fidda-Kai Ta Hau Kansu
Sheikh Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Kaduna, ya bayyanawa BBC cewa:
Zakkar Fidda-Kai wajib ce ga duk wani Musulmi da ya kai matakin wadata, komai jinsinsa (namiji ko mace) da shekarunsa (yaro ko babba).
Mutum zai fitar da ita a kansa da kuma mutanen da yake ciyarwa, kamar iyalansa.
Idan mutum yana da wadata da abinci ko da kudin da zai iya saya, dole ne ya fitar da ita.
Ga marayu, za a iya fitar da zakkar daga dukiyarsu ko kuma daga kyaututtuka da ake ba su.
Idan ‘ya’yan mutum maza sun balaga kuma suna da lafiya, ba lallai ya ci gaba da fitar musu da zakka ba.
Amma idan ‘ya’yan mutum mata ne, zai ci gaba da fitar musu har sai sun yi aure, sannan mazajensu su dauki nauyin fidda musu zakkar.
Tasirin Zakkar Fidda-Kai a Al’umma
Sheikh Halliru Maraya ya bayyana wasu mahimman fa’idodin Zakkar Fidda-Kai, ciki har da:
1. Tabbatar da wadatar abinci – Yana taimakawa wajen tabbatar da cewa kowane musulmi yana da abincin bikin Sallah.
2. Tsarkake azumi – Ana amfani da ita wajen kankare kurakuran da mutum ya aikata yayin azumi.
3. Kara zumunci – Tana karfafa soyayya da hadin kai a tsakanin musulmai.
Yadda Ake Fitar da Zakkar Fidda-Kai
Sheikh Maraya ya bayyana cewa ana fitar da ita daga nau’in abinci da al’umma suka fi ci.
Misali, idan garin kwaki ake ci a gari, mutum zai fitar da zakka da shi.
Ana fitar da Sa’i daya (mudu hudu), wanda yake daidai da kilogiram 2.5 na abinci kamar shinkafa, gero, ko dawa.
Idan za a fitar da kudi, to ya zama daidai da kudin sayen wannan nauyin abinci.
Lokacin Fitar Da Zakkar Fidda-kai
Mazhabobi sun banbanta dangane da lokacin fitar da ita:
Shafi’iyya – Ana iya fitar da ita tun daga farkon Ramadan.
Malikiyya da Hambaliyya – Sun ce ana fitar da ita kwanaki daya ko biyu kafin Sallah.
Hanafiya – Sun fi karkata ga cewa dole ne a fitar da ita kafin a yi Sallar Idi.
Idan har mutum bai fitar da ita kafin Sallar Idi ba, to duk abinda ya bayar daga baya zai zama sadaka kawai, ba zakkar fidda-kai ba. Wannan shi ne dalilin da yasa ake jinkirta Sallar Idi, domin mutane su samu damar fitar da zakkar kafin lokacin ya kure.
Zakkar Fidda- tana da matukar muhimmanci ga musulmi, kuma wajibi ne ga duk wanda yake da hali ya fitar da ita kafin sallar Idi. Ana fitar da ita domin taimakawa mabukata, tsarkake azumi, da tabbatar da zaman lafiya da jin dadin al’umma.
