Connect with us

News

Boko Haram Na Sake Mamaye Wasu Yankuna A Borno — Gwamna Zulum

Published

on

images

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan ta’addan Boko Haram ke kara yawan hare-hare da kuma mamaye wasu yankuna na jihar, yana mai cewa hakan alama ce da ke nuna cewa ana ci gaba da yaƙi a jihar.

Gwamnan ya fadi haka ne yayin wani Taron Tsaro na Musamman da ya jagoranta a babban birnin jihar, Maiduguri, inda ya ce hare-haren baya-bayan nan da garkuwa da mutane kusan kullum ba tare da matakin gaggawa ba, na barazana ga tsaron rayuka da dukiyoyi.

Advertisement

Kotu Ta Daure Ango Amuscap Wata 6 Saboda Wulakanta Naira A Bikinsa

Hare-Haren da ke Fatattakar Jami’an Tsaro

A cewarsa, hare-haren da suka faru a Wajirko da Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a Gwoza sun janyo asarar rayuka da dama ciki har da fararen hula da jami’an tsaro. “Hakan babban koma baya ne ga jihar Borno da dukan yankin arewa maso gabas,” in ji shi.

Advertisement

 

Gwamnatin Tarayya na Kokari – Zulum

Advertisement

Zulum ya yaba da irin goyon bayan da gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ke bayarwa, da kuma irin sadaukarwar jami’an tsaro, sai dai ya jaddada bukatar kara kayan aiki na zamani da kuzari wajen yaki da ta’addanci, musamman a yankunan da ke iyaka da kasashen Chadi, Nijar da Kamaru.

“Jihar Borno na fuskantar yakin da bai kamata a lamunce masa ba,” in ji gwamnan. Ya kara da cewa gwamnati ta na cigaba da tallafawa sojoji da hukumomin tsaro domin kare rayukan al’umma da kawo zaman lafiya.

Advertisement

 

Wasu Yankuna Har Yanzu Na Hannun Boko Haram

Advertisement

Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Garbai El-Kanemi, ya bayyana damuwarsa kan yadda har yanzu kananan hukumomin Guzamala, Marte, Abadam da wani yanki na Mobbar ke karkashin ikon Boko Haram. Ya ce yawancin wadannan yankuna babu shugabanni, lamarin da ke haifar da koma baya.

Shehun ya roki gwamnatin tarayya da ta gaggauta gyaran muhimman hanyoyin mota da suka hada da: Biu–Damboa–Maiduguri, Maiduguri–Dikwa–Ngala, Maiduguri–Monguno–Kukawa, da Biu–Damaturu, domin saukaka zirga-zirga da karfafa tsaro.

Advertisement

Taron ya samu halartar manyan jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki, inda aka tattauna hanyoyin da za a bi don dakile ci gaba da farmakin ‘yan ta’adda da tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending