Connect with us

News

Bindigogi 15 Da Harsashi 102: Yansanda Sun Tarwatsa Wurin Kera Makamai A Kano 

Published

on

IMG 20250414 WA0022

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta bayyana nasarar da ta samu wajen gano wani haramtaccen wurin hada makamai a unguwar Dorayi Babba da ke cikin birnin Kano, lamarin da ya kai ga kama mutane uku da kuma kwato bindigogi kirar gida guda 15 da harsashi 102.

Wadanda ake zargi da hannu a cikin wannan aiki sun hada da Abdul Sadiq, mai shekaru 43; Ahmad Muazu, mai shekaru 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40. An cafke su ne a ranar 10 ga watan Afrilu, bisa sahihan bayanan sirri da suka kai ga wannan nasarar da rundunar ta samu.

Advertisement

Sabon Hari A Filato Ya Lakume Rayukan Mutane 40

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa ga manema labarai. Ya bayyana cewa rundunar ta gudanar da bincike mai zurfi tare da hadin gwiwar jami’an tsaron jihar Kano, wanda hakan ya haifar da gano tarin haramtattun makamai.

A cewar ACP Adejobi, wannan mataki na daga cikin kokarin da rundunar ke yi na dakile yaduwar makamai marasa lasisi a fadin kasar. Ya kara da cewa hakan wani ci gaba ne mai muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Advertisement

Sufeto-Janar na ‘yansanda, IGP Kayode Egbetokun, ya yaba da kwazon jami’an da suka jagoranci wannan aiki, tare da jaddada kudirin rundunar na ci gaba da yaki da miyagun laifuka musamman kera da safarar makamai ba bisa ka’ida ba a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending