Connect with us

News

Sabon Hari A Filato Ya Lakume Rayukan Mutane 40

Published

on

AFGHANISTAN UNREST TALIBAN

Aƙalla mutane arba’in ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai da safiyar Litinin a ƙauyukan Zike da Kimakpa, da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar Bassa, Jihar Filato.

Wakili Tongwe, wani shugaban al’ummar Kwall, ya bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyukan da misalin ƙarfe 5:00 na safe, inda suka fara harbi ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya jefa mazauna cikin firgici da gudun ceton rai.

Advertisement

NOA Ta Bankado Badakala: Jami’o’i Da Bankuna Na Zaluntar Dalibai Kan Bashin Ilimi

Tongwe ya shaida wa Channels TV cewa yana tare da wata tawagar ‘yan banga da jami’an tsaro suna sintiri a wani ƙauye lokacin da suka samu kiran gaggawa dangane da harin. Duk da cewa jami’an tsaro sun yi artabu da maharan tare da korar su daga ƙauyukan, mutane 36 sun mutu a harin kai tsaye, yayin da wasu huɗu suka ce ga garinku a asibiti sakamakon munanan raunukan da suka samu.

Wasu daga cikin mazauna sun tsira da raunukan harbin bindiga kuma ana ci gaba da kula da su a asibitoci daban-daban.

Advertisement

Wannan hari ya faru ne kasa da makonni biyu bayan makamancin hare-hare a ƙananan hukumomin Bokkos, wanda suka yi sanadin mutuwar mutane 52, lamarin da ke ƙara tsananta fargaba da rashin kwanciyar hankali a yankin.

Hukumomin tsaro na jihar har yanzu ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da wannan hari. Al’umma dai na cigaba da kiran gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikice-rikicen tsaro.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending