Connect with us

News

Kwankwaso Ba Zai Koma APC Ba – Cewar Buba Galadima

Published

on

Dr. Rabiu Musa Kwankwaso

Fitaccen jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar da ke yaduwa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar APC.

A wani jawabi da ya yi wa The Guardian, Galadima ya bayyana cewa babu wata manufa ko shirye-shiryen da Kwankwaso ke yi na sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, yana mai cewa “babu mai hankali a Kano ko ko’ina a Najeriya da zai yi alfahari da kasancewa cikin APC karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje.”

Advertisement

‎ “DSP Barau: Gwarzon Majalisa Da Ke Hada Gwiwa Da Gwamnati Don Ci Gaban Kasa”

Wannan martani na Galadima na zuwa ne makonni bayan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi ikirarin cewa Kwankwaso na shirin dawowa jam’iyyar APC. Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da kungiyar Tinubu Support Group ta kai masa ziyara a Abuja, inda ya ce jam’iyyar APC na ci gaba da karbar fitattun ’yan siyasa daga sassa daban-daban na kasar.

Sai dai a cewar Galadima, “To daga gare ku na fara jin wannan magana. Idan ma za mu koma APC, Ganduje ne zai sanar da ’yan Najeriya? Saboda Ganduje kadai ma, babu wanda zai so komawa APC.”

Advertisement

Ya kuma zargi shugaban jam’iyyar APC da kokarin amfani da suna da tasirin NNPP domin neman farin jini da daukaka a kafafen yada labarai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending