News
Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC da NECO Su Koma Gudanar da Jarabawa ta Kwamfuta
Gwamnatin Tarayya ta umarci Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) da Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) da su fara gudanar da jarabawarsu ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa (Computer-Based Test – CBT) daga shekarar 2026.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin da ya kai ziyara domin sa ido kan yadda ake gudanar da jarabawar JAMB a cibiyar Bwari, Abuja.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), fiye da dalibai miliyan biyu ne suka yi rajistar jarabawar JAMB da ake gudanarwa a sama da cibiyoyi 800 a fadin kasar.
Dakta Alausa ya bayyana cewa tun daga watan Nuwamba 2025, WAEC da NECO za su fara gwada amfani da tsarin CBT ta hanyar gudanar da bangaren tambayoyi (objective) na jarabawarsu da kwamfuta. Ya ce, daga watan Mayu ko Yuni na shekarar 2026, za a fara gudanar da duka bangarorin jarabawa — tambayoyi da rubutu — ta hanyar na’ura mai kwakwalwa gaba ɗaya.
“Idan JAMB na iya gudanar da jarabawar CBT ga fiye da dalibai miliyan 2.2 cikin nasara, to babu dalilin da zai hana WAEC da NECO yin hakan,” in ji Ministan.
Ya kara da cewa wannan mataki zai taimaka matuka wajen rage yawaitar magudin jarabawa da kuma tabbatar da inganci da gaskiya a tsarin gudanar da jarabawa a Najeriya.
