Masarautar Saudiyya ta ce an sallamo Sarki Salman bin Abdulaziz daga asibiti.
Wata sanarwa da Masarautar ta fitar ta ce: “Mai yi wa Masallatai Biyu Masu Tsarki hidima, Sarki Salman bin Abdulaziz (Allah ya cigaba da kare shi) ya bar asibitin kwararru na Sarki Faisal a Riyadh bayan da likitoci suka yi nasarar binciken lafiyarsa da safiyar yau, godiya ta tabbata ga Allah.”
A watan Yulin 2020 an kwantar da Sarki Salman a asibiti na tsawon kwana 10 domin cire ma sa wasu duwatsu a jikinsa.
Shafin sada zumunta na Haramain Sharifain ya wallafa wasu hotunan sarkin mai shekara 86 yayin da yake fitowa daga asibitin, kuma ana iya ganin dansa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman cikin masu yi ma Sarkin hidima suna raka shi.


