News
NUJ Ta Bukaci Kwamishinan Lafiya Ya Ƙarfafa Yaƙi Da Cutar Zazzabin Cizon Sauro A Kano
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kano, ta nuna damuwa matuƙa kan yadda cutar zazzabin cizon sauro ke ƙara yaduwa da barazana ga lafiyar al’umma, musamman a yankunan karkara da kuma birane.
A wani babban taron da kungiyar ta gudanar ranar 29 ga Afrilu, 2025, tare da halartar wakilai daga dukkan rassan NUJ a jihar, an bukaci Gwamnatin Jihar Kano, musamman Ma’aikatar Lafiya, da ta dauki matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar.
Yunƙurin Rusa Jam’iyyun Adawa Babbar Barazana Ce Ga Dimokuraɗiyyar Najeriya — Farfesa Kamilu
Bayan taron, kungiyar ta fitar da wata sanarwa inda ta bukaci Kwamishinan Lafiya na jihar da ya samar da hanyoyi masu inganci da nagarta wajen yaki da sauro da cutar da suke haddasawa.
“Ya kamata gwamnati ta gaggauta daukar matakai kamar feshin magungunan kashe sauro, rabon gidajen sauro da magunguna kyauta, da kuma wayar da kan jama’a kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar,” in ji sanarwar.
NUJ ta jaddada cewa kare lafiyar al’umma nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati, tare da kiran a hada kai da kungiyoyin fararen hula domin samar da mafita mai dorewa kan wannan matsala da ke barazana ga rayuka da tattalin arzikin al’umma.
