News
Budaddiyar Wasika Ga Shehu Adamu: Hukumar Shari’a Ta Ce Zarginka Bai Da Tushe
Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta mayar da martani ga wani mai suna Shehu Adamu, wanda ya bayyana kansa a matsayin na’ibin masallacin gidan gyaran hali da tarbiyya na Gwauron Dutse, bisa zargin da ya yi cewa ana aikata lalata da wasu daurarru a cikin gidan.
A cikin wata budaddiyar wasika da hukumar ta fitar, wadda Mukaddashin Daraktan Wayar da Kai na hukumar, Musa Ahmad D/iya (Best Seller), ya sanya wa hannu, an bayyana cewa hukumar ta gudanar da cikakken bincike kan zargin, amma ba ta samu wani hujja da ke tabbatar da sahihancinsa ba.
“Mun gayyato limaman gidan tun da kake cewa kai na’ibinsu ne, mun kuma yi tambayoyi ga kakakin gidan. Haka zalika, mun kafa tawagar bincike ta musamman da ta shiga gidan don gudanar da bincike kai tsaye, amma cikin ikon Allah ba mu samu wani abu da ya tabbatar da zarginka ba,” in ji wasikar.
Hukumar ta kara da cewa sun duba rijistar gidan daga lokacin da ake zargi, har zuwa ranar da Shehu Adamu ya ce ya fita daga gidan, wato 29 ga Afrilu, amma ba su ga sunansa a ciki ba. Haka kuma, dakin da ya ce ya zauna an shiga an gudanar da bincike, amma babu wata alama da ke nuna abin da ya ke ikirari.
“Shugaban gidan gyaran hali da kansa ya bayyana cewa tun da ya fara aiki a gidan yana zama a bayan liman a masallacin gidan, amma bai taɓa ganin Shehu Adamu ba balle ya sance shi,” in ji hukumar
Saboda haka, hukumar ta bukaci Shehu Adamu da ya bayyana a ofishinta domin bayar da karin bayani kan zargin da ya yi. Hukumar ta ce an kira lambar wayarsa amma ba a same shi ba, don haka ta nemi duk wanda ya san shi da ya isar masa da wannan sako.
“Za a same mu a ofishin Hukumar Shari’a ta Jihar Kano da ke lamba 1, titin Abdullahi Bayero, Kano,” in ji hukumar.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
