News
Ingila Ta Rage Tsawon Lokacin Bizar Aikin Bayan Kammala Karatu Watanni 18.
Gwamnatin ƙasar Ingila ta rage tsawon lokacin bizar aikin bayan kammala karatu daga shekaru biyu zuwa watanni 18.
Wannan biza da aka fi sani da Graduate Route Visa, na bai wa ɗaliban ƙasashen waje damar yin aiki a Ingila bayan kammala karatu. Sai dai gwamnati ta ce an fara amfani da shirin ta hanyoyin da ba su dace ba.
Gwamna Abba Ya Dauki Masu Gadi 17,600 Don Bai Wa Makarantun Jihar Tsaro
A wata takarda da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar a ranar Litinin, gwamnati ta ce: “Shirin Graduate Route bai cika manufofinsa na farko ba, kuma yanzu yana zama wata hanya da ake bi don samun aikin da ba a shirya masa ba.”
Sabon tsarin ya ƙara tsaurara hanyoyin da ɗalibai ke bi wajen samun aiki na dindindin, tare da hana su kawo ‘yan uwansu daga gida bayan karatu.
Haka kuma, jami’o’in da za su ci gaba da karɓar ɗaliban ƙasashen waje dole ne su cika ƙa’idojin da aka sabunta. Idan jami’a ta karya ƙa’ida ko ɗalibanta sun kasa samun aiki bayan karatu, za a ɗauki mataki a kanta.
Wannan mataki na daga cikin gyare-gyaren da gwamnati ke yi don hana amfani da shirin karatu a matsayin hanyar neman mafaka da kuma daƙile cin hanci a cikin tsarin.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
