Connect with us

News

UTME 2025: Dalibai 379,997 Ne Za Su Sake Zama Jarabawar JAMB

Published

on

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun gaba da Sakandare (JAMB) ta ce dalibai 379,997 ne za su sake rubuta jarabawar UTME ta bana saboda matsalolin da suka taso a lokacin gudanar da jarrabawar a wasu jihohin kasar nan.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai da ya yi a birnin Abuja ranar Laraba.

Advertisement

Yadda Wasu Ke Yunkurin Sayar Da Filin Makarantar ’Yan Mata A Kano

Ya ce matsalolin sun fi kamari ne a wasu cibiyoyi da ke Jihohin Kudu Maso Gabas da kuma Legas, inda aka samu tangarda wajen gudanar da jarrabawar.

Farfesa Oloyede ya ce tun daga ranar Alhamis za su fara tura sakonnin waya ga daliban da abin ya shafa domin sanar da su ranar da za su sake rubuta jarabawar.

Advertisement

Ya ce, “Mun dauki alhakin matsalolin da suka faru, kuma muna neman afuwar iyaye da dalibai. Mun dauki matakan da suka dace domin ganin hakan bai sake faruwa ba a gaba.”

Kashi 75 Cikin 100 Sun Kasa Kai Maki 200

Advertisement

A bana dai, dalibai miliyan daya da dubu dari tara da hamsin da biyar da saba’in da tara (1,955,079) ne suka rubuta jarabawar UTME a fadin kasar.

Sai dai kuma, bayan fitar da sakamako, ya bayyana cewa fiye da kashi 75 cikin 100 na daliban sun kasa kai maki 200 daga cikin 400, wanda shi ne mafi rinjaye da ake duba wajen samun gurbin karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu.

Advertisement

Ga yadda sakamakon ya kasu:

Dalibai 4,756 ne suka samu maki daga 320 zuwa sama

Advertisement

7,658 sun samu daga 300 zuwa 319

73,441 sun samu daga 250 zuwa 299

Advertisement

334,560 sun samu daga 200 zuwa 249

983,187 sun samu daga 160 zuwa 199

Advertisement

488,197 sun samu daga 140 zuwa 159

57,419 sun samu daga 120 zuwa 139

Advertisement

3,820 sun samu daga 100 zuwa 119

2,031 ne kadai suka kasa samun maki 100

Advertisement

Wannan sakamako ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin iyaye da malamai, inda da dama ke ganin akwai bukatar JAMB ta sake duba tsarin gudanar da jarabawar da kuma irin sakamakon da take bayarwa.

Wasu na ganin rashin isasshen shiri da horo na dalibai da kuma matsalolin cibiyoyin jarrabawa sun taka rawa wajen faduwar da aka samu.

Advertisement

 

 

Advertisement

Platinum Post

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending