News
Kwaddibuwa Na Cikin Rudani Bayan Harbe-harbe Da Zanga-zanga
Ana ci gaba da rade-radin cewa sojoji sun kwace mulki a Jamhuriyar Kwaddibuwa, inda ake zargin sun hambarar da gwamnatin Shugaba Alassane Ouattara.
Jita-jitar ta fara karade sassa daban-daban na kasar tun bayan jin karar harbe-harbe a babban birnin kasar, Abijan, da wasu manyan birane. Wannan ya kara tada hankalin jama’a da kuma janyo zaman dar-dar.
Wasu rahotanni na cewa an samu zanga-zanga da rikici a Abijan, inda mutane fiye da 30 suka rasa rayukansu a cikin kwanaki biyu, bisa ga abin da majiyoyi suka bayyana.
Sai dai zuwa yanzu, babu wata tabbatacciyar sanarwa daga hukumomi ko wata majiyar da za ta iya tabbatar da juyin mulkin. Bugu da kari, yanke intanet a wasu yankunan kasar ya sa samun bayanai na gaskiya ya zama ƙalubale.
Har ila yau, ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan inda Shugaba Ouattara yake. Wasu na cewa an kama shi, wasu na ganin ya tsere, yayin da wasu ke rade-radin cewa ya rasu. Amma duk wannan magana ce babu tabbas.
A gefe guda kuma, an gano cewa wasu daga cikin bidiyoyin da ke yawo a shafukan sada zumunta ba su da alaka da Kwaddibuwa – wasu tsofaffi ne, wasu kuma daga wasu kasashe ne aka samo su.
Wannan ba shi ne karon farko da ake jin irin wannan jita-jita ba. A baya-bayan nan an sha samun rade-radin juyin mulki, musamman daga masu sukar Ouattara da ke ganin yana da kusanci da Faransa, tsohuwar mai mulkin mallaka.
Muna ci gaba da bin diddigin labarin kuma za mu rika kawo muku gaskiyar abin da ke wakana daga Kwaddibuwa in dai lokaciya ba mu dama.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
