News
Farfesa Gwarzo Ya Yaba Wa Shugaban Jami’ar Nile Kan Inganta Ilimi Da Bincike
Shugaban Kungiyar Jami’o’in Kudi na Nahiyar Afrika (AAPU), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya yi yabon ci gaban da jami’ar Nile ta samu a fannin ilimi da bincike, inda ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin jami’o’in Afrika domin bunkasa tsarin karatu da warware matsalolin da ke addabar nahiyar.
A yayin ziyarar aiki da ya kai jami’ar a Abuja, Farfesa Gwarzo ya bayyana cewa hadin kai tsakanin jami’o’i zai taimaka wajen kawo sauyi mai dorewa, ba kawai a fannin ilimi ba, har ma a bangaren tattalin arziki.
Gwamnatin Kano Za Ta Fitar Da Sama Da Naira Biliyan 20 Don Ayyuka A Fadin Jihar
“Abin alfahari ne ganin wani shugaban jami’a dan Najeriya yana jagorantar wannan ci gaba mai matukar tasiri,” in ji Farfesa Gwarzo. “Ba wai kawai kara yawan dalibai ko gina sabbin gine-gine bane, amma inganta tsarin koyarwa wanda ke baiwa dalibai damar magance matsaloli na gaske.”
“Idan jami’o’i ba su hada kai ba, to za mu ci gaba da fuskantar kalubale masu tsanani a nahiyar,” in ji shi.
A nasa bangaren, Shugaban Jami’ar Nile, Farfesa Dilli Dogo, ya tabbatar da cewa jami’ar za ta ci gaba da bude kofa ga duk wata hadin gwiwa wadda za ta kawo ci gaba da samar da sakamako mai amfani ga dalibai da al’umma baki daya.
