News
NUJ Ta Bukaci Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Manoma Kafin Damina
Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen kafafen intanet na Jihar Kano, ta roƙi Gwamnatin Jihar Kano ta taimakawa manoma da iri da kayan aikin noma kafin a shiga damina.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na farko, wanda aka gudanar a karshen mako.
Shirin Ƴan Adawa Na Kawar Da Tinubu A 2027 Ya Fara Tangal-tangal
Sanarwar da Shugaban kungiyar, Abubakar Abdulqadir Dangambo, da Sakatare, Isiyaku Ahmed, suka sanya wa hannu, ta bukaci gwamnati ta gaggauta gyara hanyoyin karkara da na al’umma don sauƙaƙa zirga-zirga a lokacin damina.
> “Taron ya gudana tare da wakilan kafafen watsa labarai daban-daban da ke aiki ta yanar gizo a jihar,” in ji sanarwar.
Dangambo ya yaba wa mambobin kan yadda suka haɗa kai wajen kafa sabon reshen, tare da jaddada muhimmancin aiki da ƙa’idojin aikin jarida da rikon gaskiya wajen watsa labarai.
