News
Fusatattun Matasa Sun Cinna Wuta A Ofishin ‘Yan Sanda Na Rano
Ana zaman zullumi a garin Rano da ke Jihar Kano, bayan da wasu matasa suka kai farmaki ga ofishin ‘yan sanda na garin tare da cinna masa wuta, biyo bayan zargin mutuwar wani matashi da aka kama.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren Asabar, bayan da aka wayi gari da labarin mutuwar matashin a hannun ‘yan sanda. Wannan ya fusata wasu matasa da suka taru suka nufi ofishin ‘yan sandan, inda suka kona wani bangare na ginin.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “An kama matashin ne saboda zargin addabar mutane da kwace kudinsu da karfin tsiya da karagar babur, sai dai ba da dadewa ba aka ji cewa ya mutu a ofishin.”
Lamarin ya jefa jama’a cikin fargaba, inda da dama suka rufe shagunansu, yayin da ‘yan sanda suka bazama cikin gari domin hana karin tarzoma.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an fara bincike kuma za a dauki matakin da ya dace kan wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Ya ce, “Rundunar ba za ta lamunci daukar doka a hannu ba. Zamu bi dukkan matakan da suka dace don tabbatar da doka da oda.”
A halin yanzu dai, har yanzu ana ci gaba da tsaurara matakan tsaro a garin, yayin da jama’a ke ci gaba da zaman dar-dar.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
