News
Kano Ta Zama Cibiyar Bincike Da Maganin Cututtuka Na Zamani — Farfesa Salihu
Darakta Janar na Cibiyar Bincike Mai Zaman Kanta ta Kano (KIRCT), Farfesa Hamisu Salihu, ya bayyana cewa jihar Kano na kan gaba a bangaren bincike da gano cututtuka ta hanyar amfani da sabbin na’urori da fasahohin zamani da ke taimakawa wajen gano cuta da kuma samar da magani da ya dace da kowanne mutum.
Farfesa Salihu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin duba ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a cibiyar da ke Kwanar Dawaki, a karamar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano, a ranar Talata.
Ya ce, tare da shigar da na’urori na zamani irin su Next Gen 2000, cibiyar za ta taimaka gaya wajen gano cututtuka masu tsanani kamar kansar mama da sauran ire-irenta, ta yadda za a iya samar da magani da ya dace da kowanne irin nau’in cutar.
“Next Gen 2000, wadda ita ce irinta ta farko a Arewacin Najeriya, tana iya gano kwayar halittar kowanne irin kansa. Wannan zai taimaka wajen tantance nau’in cutar, sannan kuma mu samar da magani da ya dace. Ci gaba ne wanda zai taimaka wajen ceto rayuka,” in ji shi.
A cewarsa, akwai kuma na’urori irin su MI SEQ 1100+, B2 Solo – DNA, da kuma fasahar zamani ta pharmacogenomics, wadanda ke bai wa cibiyar damar gano tushen cututtuka da tsara magani bisa kwayoyin halittar mutum, maimakon amfani da irin magani daya ga kowa.
“Mun shiga sabon zamani ne da ke bayar da damar kula da lafiya bisa bukatun jikin mutum. Wannan ya fi amfani kuma yana rage kashe kudade, tare da kara kudaden shiga da inganta tsarin lafiya,” Farfesa Salihu ya bayyana.
Ya kara da cewa cibiyar ta riga ta janyo hankalin hukumomi da dama ciki har da Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) da wasu hukumomin tarayya, wadanda suka nuna niyyarsu ta turo jami’ansu domin koyon dabarun amfani da fasahar genomics surveillance.
A yayin zagayen, an bayyana cewa cibiyar na da asibiti na zamani da ke karbar marasa lafiya, inda ake ba su kulawa ta musamman ta hanyar amfani da sabbin na’urori da kayan aiki na zamani.
Farfesa Salihu ya jaddada cewa wannan ci gaba da Kano ke samu zai kara janyo hankalin masana da kwararru daga sassa daban-daban na kasar, da nufin ganin an kafa wata sabuwar hanya ta bincike da magance cututtuka bisa ilimi da fasahar zamani.
