Connect with us

News

Ginin Makaranta Ya Rufta A Lokacin Jarabawa A Taraba

Published

on

FB IMG 1748530044286

Daruruwan ɗalibai sun tsallake rijiya da baya a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne, a Ƙaramar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba, bayan da ginin ajujuwan da ake gudanar da jarabawar kammala sakandare (SSCE) ya rufta yayin da suke cikin rubuce-rubuce.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Laraba, lokacin da ruwan sama mai ƙarfi da iska suka mamaye yankin. A cewar shaidu, guguwar ta tsayar da ajujuwan ginin makarantan har suka rufta a bisa ɗalibai da masu kula da jarabawa.

Advertisement

Kaɗan Daga Cikin Jawabin Da Shugaba Tinubu Ya Yi Kan Cikarsa Shekaru 2 A Mulki

Wani mazaunin garin, Alhaji DanAzumi Lauris, ya bayyana wa Daily Trust cewa wannan shine karo na biyu da irin wannan hatsari ke faruwa a makarantar. Ya ce rukuni na farko na ɗalibai ya gama jarabawa kafin ginin ya rufta, amma rukuni na biyu na ciki a lokacin da lamarin ya afku.

“Mun yi ta kokarin ceto ɗaliban da suka maƙale, kafin mazauna garin su samu damar kai musu dauki,” in ji DanAzumi.

Advertisement

An garzaya da waɗanda suka jikkata – ciki har da ɗalibai, malamai da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) – zuwa cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko da ke kusa da makarantar, inda suke ci gaba da samun kulawa.

Baya ga makarantar, guguwar da ta haddasa ruftawar ginin ta kuma lalata gidaje da dama a cikin unguwar Namne.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending