Connect with us

News

EFCC Ta Cafke Mutum Biyu Da Dala $899,800 Na Ƙudin Ɓogi A Kano

Published

on

1748700270818

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) reshen Kano ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da mallakar kuɗin bogi har dala $899,800, wanda kimar kuɗin ta kai kusan Naira miliyan 1.3 a kasuwar yau.

Advertisements
Advertisements

An kama waɗanda ake zargin ne a kan titin Maiduguri Road, cikin garin Wudil na jihar Kano, yayin da suke cikin wata mota kirar Golf 3. Rahotanni sun bayyana cewa an gano kuɗin a cikin kwalayen Maggi da aka ɓoye su a ciki.

Advertisements

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Kotu Ta Musamman Don Hukunta Masu Satar Amsa 

EFCC ta bayyana cewa waɗanda ake zargin sun bayyana cewa su na kan hanyarsu ce ta zuwa garin Kila, a jihar Jigawa, domin haɗuwa da wani boka da ya sha alwashin zai canza kuɗin bogi zuwa na gaskiya ta hanyar addu’o’i da wasu hanyoyi na sihiri.

Advertisements
Advertisements

A cikin wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook, EFCC ta ce bincike ya na ci gaba, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending