News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Kotu Ta Musamman Don Hukunta Masu Satar Amsa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce tana shirin kafa kotu ta musamman da za ta rika shari’ar masu laifin satar amsa da sauran nau’ikan magudin jarrabawa a fadin ƙasar.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja yayin da yake karɓar rahoton kwamitin musamman da aka kafa domin inganta tsarin gudanar da jarrabawa a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede na Hukumar JAMB.
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 21 Daga Tawagar Wasannin Kano
Ministan ya ce gwamnati za ta aiwatar da duk shawarwarin kwamitin guda 12, da nufin tabbatar da sahihancin jarrabawa da ingancin ilimi a matakin ƙasa.
“Za mu kafa wannan kotu ne domin hukunta masu laifin magudi a jarrabawa, kuma hakan zai zama izina ga sauran dalibai da malamai da ke shiga irin waɗannan ayyuka,” in ji Minista Alausa.
Ya kara da cewa gwamnatin za ta yi amfani da kowane mataki da ya dace wajen dakile wannan matsala da ke ƙalubalantar amincin sakamakon jarrabawa a Najeriya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar yadda satar amsa da magudin jarrabawa ke kara karfi a cibiyoyin jarabawa, musamman a lokutan WAEC, NECO da JAMB.
