Connect with us

News

Wata Mahajjaciya Daga Najeriya Ta Rasu A Makkah

Published

on

Hajjin ban

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya daga jihar, Hajiya Jamila Muhammad, a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Sakataren gudanarwa na hukumar, Malam Daiyabu Dauda, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a ranar Talata, a Jos, babban birnin jihar.

WhatsApp Zai Daina Aiki A Kan iPhone 6, Galaxy S4 da Wasu Wayoyin Guda 11

Dauda ya ce Hajiya Jamila ta rasu ne a ranar Litinin a asibitin Sarki Abdul’aziz da ke Makkah, bayan fama da matsanancin ciwon suga (diabetes).

“Da zarar alamomin cutar suka bayyana, muka gaggauta kai ta asibiti domin samun kulawa ta gaggawa, kamar yadda tsarinmu ya tanada,” in ji shi.

Sai dai, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi, Allah Ya karɓi rayuwarta. Likitan da ya duba ta ya tabbatar da cewa cutar suga ce ta yi sanadin rasuwarta.

Sakataren ya ƙara da cewa an binne marigayiyar a Makkah, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Advertisement

Ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamaciyar, tare da roƙon Allah Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa danginta haƙurin jure wannan babban rashi.

 

 

NAN

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending