Connect with us

News

Gwamnatin Yobe Ta Rufe Makarantu Na Kwanaki 10

Published

on

Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da rufe dukkan makarantun gwamnati da na ƙashin kai a faɗin jihar na tsawon kwanaki goma, domin bai wa ɗalibai da malamai damar gudanar da bukukuwan Babbar Sallah cikin natsuwa da lumana.

Sanarwar rufe makarantun za ta fara aiki daga Laraba, 4 ga Yuni, 2025, zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025, kamar yadda wata takarda mai ɗauke da sa hannun Daraktan Kula da Makarantu, Bukar Modu, a madadin Kwamishinan Ilimi na jihar, ta tabbatar.

Advertisement

Wata Mahajjaciya Daga Najeriya Ta Rasu A Makkah

Hutun ya yi daidai da lokacin da Majalisar Manyan Malaman Addinin Musulunci ta Najeriya ta ayyana Juma’a, 7 ga Yuni, 2025 a matsayin ranar Sallar Idi, tare da zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya da za a gudanar a ranar Laraba, 12 ga Yuni, 2025.

Ma’aikatar Ilimi ta umarci dukkanin makarantun da su bi umarnin nan kai tsaye, domin samar da lokacin hutu mai armashi ga ɗalibai, malamai da iyayensu.

Advertisement

Kwamishinan Ilimi na jihar, Farfesa Adam Idris, ya yi fatan alheri ga al’ummar jihar Yobe baki ɗaya a lokacin bukukuwan, yana mai jaddada buƙatar iyaye da su ɗauki nauyin kula da ’ya’yansu yadda ya kamata kafin, yayin, da kuma bayan bukukuwan sallah.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending