Connect with us

News

Falaloli 12 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Arafa

Published

on

Dutsen Arfa

Ranar Arafa na daya daga cikin manyan ranaku masu albarka a shekarar Musulunci, musamman a cikin kwanaki goma na farkon watan Zulhijja. Wannan rana tana dauke da dimbin lada da falala kamar yadda hadisan Manzon Allah (SAW) suka tabbatar.

Ga wasu daga cikin muhimman falalolin wannan rana:

Rundunar yansanda a Kano ta sanar da hana Hawan sallah a jihar

1. Rana mafi falala a shekara – Ranar Arafa ce mafi daukaka daga cikin sauran ranaku a duk shekara, kamar yadda hadisi ya tabbatar.

2. Allah Ya cika addini a cikinta – A wannan rana ne Allah Madaukakin Sarki Ya cika addinin Musulunci, Ya kuma gama ni’imarsa ga bayi.

3. Allah Ya yi rantsuwa da ita a cikin Alkur’ani – Wannan rana ta samu girmamawa inda Allah Ya rantse da ita a cikin Suratul Buruj.

4. Yantar bayi daga wuta – A wannan rana, Allah yana yantar da bayi masu yawan addu’a da ibada daga wuta zuwa Aljanna.

Advertisement

5. Tsayuwar Arafa – Alhazai daga sassa daban-daban na duniya sukan taru a filin Arafa domin tsayuwa, wato muhimmin rukuni na aikin Hajji.

6. Alfaharin Allah da bayinsa – A ranar, Allah na alfahari da bayinsa da suka halarci filin Arafa ga Mala’iku, yana nuna yadda suka bar komai don neman rahama.

7. Tsayuwar Arafa ita ce Hajji – Manzon Allah (SAW) ya ce: “Alhajju Arafah”, wato duk wanda bai tsaya a Arafa ba, aikin Hajjin sa bai inganta ba.

8. Azumi ga wadanda ba sa Hajji – Azumtar Ranar Arafa yana kankare zunuban shekara guda da ta gabata da kuma shekara mai zuwa, kamar yadda hadisi ya bayyana.

9. Rana mai albarka da tanadi ga Aljanna – Falalar wannan rana na daga cikin hanyoyin samun gafara da samun shiga Aljanna.

10. Hudubar bankwana – A wannan rana ce Manzon Allah (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta bankwana, wadda ta kunshi muhimman koyarwa ga al’ummar Musulmi.

Advertisement

11. Ranar da addu’a ke fi karbuwa – Wannan rana ce mafi alheri wajen karbar addu’a. Manzon Allah (SAW) ya ce addu’ar da ta fi falala a wannan rana ita ce:

“Lā ilāha illallāhu waḥdahu lā sharīka lah, lahu-l-mulku wa lahu-l-ḥamdu wa huwa ‘alā kulli shai’in qadīr.”

12. Lokacin ayyukan alheri – Wannan rana na daga cikin lokutan da ya kamata a kara yawan ayyukan alheri kamar:

Gaida marasa lafiya ,Karatun Alkur’ani, Istigfari da salati ga Annabi (SAW), Zikirai da azkar da addu’o’i.

Ranar Arafa wata dama ce ta musamman ga dukkan Musulmi – masu aikin Hajji da wadanda ba su samu damar zuwa ba. Ya kamata a yi amfani da wannan rana wajen neman gafara, azumi, addu’a da sauran ayyukan alheri domin samun falalar da ke tattare da ita.

 

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending