News
Ambassador Dr. Umar Shu’aibu Gwarzo Ya Taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Murnar Babbar Sallah
Ambassador Dr. Umar Shu’aibu Gwarzo ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da daukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin Babbar Sallah.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Ambassador Gwarzo ya bayyana cewa lokacin Sallah wata dama ce ta godiya ga Allah da kuma tunawa da manyan darussa na biyayya, hadaya da sadaukarwa da ke kunshe a cikin labarin Annabi Ibrahim (AS).
Kwamishina Waiya Ya Yi Wa Gwamna Abba, Kwankwaso, Gwarzo Da Al’ummar Musulmi Barka Da Sallah
“Ina mika sakon fatan alheri ga Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan lokaci mai albarka. Allah Ya kara masa nasara, lafiya da jagoranci na gari,” in ji shi.
Ambassador Gwarzo ya kuma mika gaisuwar Sallah ga Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, yana mai fatan Allah Ya kara masa lafiya da kwanciyar hankali.
Haka zalika, ya taya Jagoran Kwankwasiyya na Kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso (PhD), murnar Sallah, tare da yi masa fatan alheri da karin daukaka.
Ya kuma mika sakon taya murna ga Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Isma’il Falgore, da ‘yan majalisun dokoki na jiha da na tarayya, da mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar.
“Ina mika fatan alheri ga daukacin al’ummar Jihar Kano da Musulmi gaba daya a fadin duniya. Allah Ya sanya wannan lokaci na Sallah ya kasance na hadin kai, zaman lafiya da karfafa zumunci,” in ji shi.
A karshe, Ambassador Gwarzo ya bukaci jama’a da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da natsuwa, tare da yin addu’ar zaman lafiya da ci gaban jihar Kano da Najeriya baki daya.
