News
Za’a Fara Shigar Da Kararraki Ta Hanyar Amfani Da Internet A Manyan Kotunan Tarayya
Babbar Kotun Tarayya ta Najeriya ta kaddamar da sabon tsarin zamani na shigar da kararraki ta hanyar amfani da intanet a reshen kotun dake Lagos, wanda zai fara aiki daga ranar Litinin, 23 ga watan Yuni, 2025.
Wannan sauyi na daga cikin kokarin sauya yanayin gudanar da shari’a daga tsarin gargajiya zuwa na zamani, domin rage jinkiri da kara inganta yadda ake gudanar da shari’u a kotuna.
Ambassador Dr. Umar Shu’aibu Gwarzo Ya Taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Murnar Babbar Sallah
A wata sanarwa da Babban Mai Rijista na kotun, Sulaiman Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga ranar da aka kayyade, ba za a sake karɓar kararraki ta hanyar rubuce-rubuce na hannu ba, domin komai zai koma tsarin e-filing.
Sai dai ya bayyana cewa dukkan shari’un da aka riga aka shigar kafin fara wannan tsari za a ci gaba da tafiyar da su ta hanyar tsohon tsarin har sai an kammala su.
Sanarwar ta kuma umarci lauyoyi da su tabbatar sun bude asusun ‘Legal Mail’ kafin a fara amfani da tsarin, kasancewar hakan na daga cikin sharuddan samun dama ga sabon dandamali na shigar da kara ta yanar gizo.
“Wannan asusun na Legal Mail ya zama wajibi ga kowane lauya da ke son shiga wannan tsarin,” in ji Hassan.
Babban Mai Rijistar ya kuma gargadi lauyoyi da su guji bayyana bayanai na karya ko saukaka kudaden karar da gangan, domin hakan na iya janyo hukunci.
