Connect with us

Politics

‎Kano Tana Bukatar Gwamna Wanda Ba Yaron Wani Ba, Wanda Zai Tsaya Da Kafarsa Ya Duba Alummar Jihar ‎ ‎ ‎ ‎—Inji Adnan Mukhtar

Published

on

Adnan Mukhtar
Dan gwagwarmaya a Jihar Kano, Comrade Adnan Mukhtar

Wani matashi ɗan gwagwarmaya a Jihar Kano, Comr. Adnan Mukhtar, ya bayyana cewa jihar na bukatar gwamna mai cikakken ikon kansa, wanda ba yaron wani bane a harkar siyasa.

‎A cewar Adnan, Kano na bukatar shugaba mai hangen nesa da jajircewa, wanda zai tsaya da kafarsa ya fuskanci matsalolin da al’ummar jihar ke fuskanta ba tare da dogaro da wani uba a siyasa ba.

Advertisement

Guguwa Ta Lalata Gidaje Da Dama A Kano

‎Ya ce, “Kano tana bukatar gwamna wanda ba yaron wani ba, wanda zai tsaya da kafarsa ya duba al’ummar Jihar. Kano a yanzu bata bukatar Abba ko Gawuna.”

‎Wannan furuci ya biyo bayan yadda batun mulkin jihar Kano ke ci gaba da jan hankali, musamman tsakanin jiga-jigan siyasa da magoya bayansu.

Advertisement

‎Adnan, wanda ya shahara wajen bayyana ra’ayinsa kan al’amuran siyasa da shugabanci, ya jaddada cewa lokaci ya yi da Kano za ta samu gwamna mai zaman kansa wanda zai dora jihar kan turbar cigaba mai ɗorewa.

‎Jaridar INDA RANKA ta rawaito cewa furucin nasa na ɗaya daga cikin jerin kalaman da ke bayyana matsin lamba kan bukatar samun sabbin jagorori masu kishin kasa da mutane a gaba.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending