Connect with us

News

Guguwa Ta Lalata Gidaje Da Dama A Kano

Published

on

Guguwa Ta Lalata Gidaje Da Dama A Kano

Wata guguwa mai ƙarfi da ta afku a ranar Litinin ta yi ɓarna a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Bunkure da ke Jihar Kano, inda ta rushe gidaje da dama tare da barin mazauna da dama cikin yanayi na rashin matsuguni.

Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Sakafalle-Jalabi da Zangon Buhari, duk a yankin Kulluwa, inda guguwa ta kwashe rufin gidaje da dama da aka yi da ƙarfe (zinc), tare da rushe wasu gidaje da aka gina da tubalin kasa da siminti.

Har yanzu ba a ga sama da mutum 700 ba bayan ambaliyar Mokwa — Gwamnatin Neja

Ko da yake babu asarar rai da aka samu, dukiyoyi masu yawa sun salwanta, abin da ya haddasa ƙunci da dimuwa ga mazauna yankin da lamarin ya shafa.

 

Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Bunkure, Malam Labaran Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa “ba a rasa rai ba, amma an samu asarar dukiyoyi da dama sakamakon guguwar.”

Wakilin Hakimin Bunkure, Nasiru Umar, ya ruwaito lamarin ga Sarkin Rano, Alhaji Isa Umar, wanda ya bayar da umarnin tattara cikakken rahoto domin mikawa majalisar ƙaramar hukuma don ɗaukar matakin da ya dace.

Advertisement

Sarkin ya kuma yi kira ga mazauna ƙauyukan da abin ya shafa da su ɗauki matakan kariya daga irin waɗannan masifu da ka iya aukuwa a lokacin damina.

 

 

DAILY NIGERIAN 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending