News
Bincike: Al’ummar Tassa Na Fuskantar Barazana Saboda Hakar Yashi Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
Wasu mazauna ƙauyen Tassa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano na fuskantar barazana a rayuwarsu da kuma muhallinsu, sakamakon hakar yashi ba bisa ka’ida ba da ake ci gaba da yi a yankin.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa yawan hakar yashin da ake yi ya haddasa Ruftawar kasa ,Rashin Ruwa a rijiyoyi, da kuma lalacewar ƙasar noma a yankin — lamarin da ke barazana ga amfanin gona da rayuwar al’umma.
NUJ Ta Karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf A Bikin Cika Shekaru 70
Abdulwahab Dantsoho, wani matashi mazaunin ƙauyen, ya ce tun 2007 suke kai koke-koke, amma ba a ɗauki mataki ba.
“Mun rasa bishiyoyi, ƙasa ta lalace, ruwa ya gurɓace. Gidaje na rushewa, amma babu wani matakin da gwamnati ta dauka” in ji shi.
Yahaya Hussaini ya ce rijiyar da ke gaban gidansa ta Rufta, kuma yana cikin fargaba cewa gidansa zai rushe a kansa.
“Ina tunanin barin gida gaba ɗaya saboda tsoro,” a cewarsa.
Talatu Abdulrahman, wata tsohuwar manomiya, ta ce ta rasa gonakin mangwaro har kadada uku saboda rashin ruwa da rushewar ƙasa.
Muhammad Khamis Garba, wani manomi, ya ce bishiyoyin mangwaro a gonarsa sun mutu gaba ɗaya, inda ya sare su domin amfani da su a matsayin itacen girki.
Duk da irin wadannan koke-koke, gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin jawo masu saka jari daga waje domin habaka harkar ma’adinai a jihar, ta hannun Ma’aikatar Ma’adinai da Albarkatun Ƙasa.
Sai dai mazauna ƙauyen na kallon wannan mataki a matsayin rashin damuwa da illar da hakar ke haddasawa ga rayuwarsu da lafiyarsu.
“Al’umma sun gaji da jiran taimako. Idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, to mu da kanmu za mu dauki mataki,” in ji Dantsoho.
A watan Mayun 2025, gwamnatin jihar ta fitar da gargadi ga masu hakar yashi ba tare da lasisi ba, tana umartar dakatar da hakan. Sai dai rahoton baya-bayan nan ya nuna cewa umarnin bai sauya komai ba a aikace.
