Rahotanni daga wasu kauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Bungudu ta jihar Zamfara a Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun halaka mutum sama da 15 da kuma garkuwa da wasu kusan 60.
Wasu mazauna ƙauyen da suka tsere zuwa Kauyen Bingi sun shaida wa BBC cewa an kai hari ne bayan sallar Azahar a yau Asabar.
Lamarin ya tarwatsa garuruwan biyu kuma waɗanda aka yi garkuwa da su sun haɗa da maza da mata da kuma ƙananan yara.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga harin ya yi wa Umayma Sani bayanin yadda lamarin ya faru. Sai dai ya buƙaci mu ɓoye sunansa saboda dalilai na tsaro.
