News
Mun Karɓi Buƙatar Ƙirƙirar Sabbin Jam’iyyun Siyasa Guda 110 — INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa zuwa ranar 23 ga Yunin 2025, ta karɓi takardun buƙata daga ƙungiyoyi 110 da ke neman a yi musu rajista a matsayin sabbin jam’iyyu siyasa a Najeriya.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Laraba a Abuja, yayin taron tattaunawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai.
PDP Ta Sake Mayar Da Samuel Anyanwu Matsayin Sakataren Ƙasa Na Jam’iyya
Yakubu ya ce hukumar za ta yi aiki da dukkan buƙatun cikin gaskiya da bin dokokin zaɓe.
“Mun riga mun amsa dukkan takardun da suka shigo, sai guda shida da muka karɓo kwanan nan. Nan da ƙarshen mako za mu amsa su ma,” in ji Yakubu.
INEC ta ce, domin tabbatar da gaskiya, za ta fitar da jerin sunayen ƙungiyoyin da suka nemi rajista, sunayen shugabannin rikon ƙwarya da kuma adireshinsu.
Yakubu ya musanta zargin da wasu ke yi cewa hukumar na nuna son kai wajen tantance waɗanda ke neman rajista.
Ya ce, “A shekarar 2019 muna da jam’iyyu 91 da suka shiga zaɓe da ’yan takarar shugaban ƙasa 73. Bayan zaɓen muka soke fiye da jam’iyyu 70, bisa doka.”
Yakubu ya ƙara da cewa INEC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa doka da gaskiya ga kowa.
Game da sauran shirye-shiryen hukumar, Yakubu ya ce INEC na shirin gudanar da zaɓukan cike gurbi da kuma dawo da aikin rajistar masu zaɓe (CVR).
