Connect with us

News

An Cafke Matashi Da Ya Lakadawa Mai Jego Dukan Tsiya A Minna

Published

on

cuff jail crime

Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Surajo, bisa zargin lakadawa wata mai jego, Deborah Andrew, dukan tsiya a garin Minna.

Lamarin mai cike da tashin hankali ya faru ne ranar 18 ga watan Yuni a unguwar Tunga-Goro da ke Minna, yayin da matar ke shayar da jaririnta.

Farm Centre: Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Ta Taɓa Hana Kowanne Ɗan Ƙasa Ko Ƙungiya Bayar da Gudummawa Ba

DAILY TRUST ta ruwaito cewa Surajo, wanda ke zaune a gidan haya daya da matar, ya afka dakinta kai tsaye, inda ya yi ta jibgarta ba tare da wani dalili ba, hatta jaririn da ke hannunta ma sai da ya jefa shi kasa.

Mijin Deborah ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da shi baya gida. “Matata ta kira ni tana kuka tana cewa za a kashe ta. Da na dawo gida, na tarar Surajo ya riga ya ci mata mutunci da duka,” in ji mijin.

A bangarensa, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Surajo na tsare a hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.

“Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ya haddasa lamarin. Makwabta sun tabbatar mana babu wata hatsaniya tsakanin bangarorin biyu kafin faruwar wannan abu,” in ji DSP Abiodun.

Advertisement

Rundunar ta bayyana cewa da zarar an kammala bincike, za a dauki matakin da ya dace.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending