Connect with us

News

“Mun cimma matsaya da Gwamna Fubara, mun yanke shawarar aiki tare” —Wike

Published

on

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa sun cimma matsaya tare da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, domin kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

Wike, wanda ya bayyana hakan bayan wani taron sulhu da aka gudanar a daren Alhamis a fadar shugaban kasa, ya ce bangarorin biyu sun amince za su yi aiki tare domin ci gaban jihar.

An Cafke Matashi Da Ya Lakadawa Mai Jego Dukan Tsiya A Minna

A cewarsa: “Mun yarda duka za mu yi aiki tare da gwamna, shi ma ya yarda zai yi aiki tare da mu. Mu duka iyali ɗaya ne a siyasa. Kamar yadda mutane ke samun saɓani, haka ma ake samun fahimta daga baya. Wannan ne muka zo muka sanar da Shugaban Ƙasa cewa mun daidaita. Don haka a gare ni, komai ya ƙare.”

Taron sulhun wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta, ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasar jihar, ciki har da Minista Wike da Gwamna Fubara, tare da wasu masu ruwa da tsaki daga bangarorin biyu.

An dai shafe watanni ana samun rashin jituwa tsakanin bangaren Gwamna Fubara da na tsohon ubangidansa a siyasa, Nyesom Wike, lamarin da ya haddasa tashin hankali a majalisar dokokin jihar da kuma a cikin jam’iyyar PDP reshen jihar.

Da alama dai wannan yarjejeniya za ta zame matakin farko na dawo da zaman lafiya da daidaito a harkokin siyasa a jihar Rivers.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending