Connect with us

News

Mahara Sun Sace Hakimi A Kaduna

Published

on

AFGHANISTAN UNREST TALIBAN

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki kauyen Bauda da ke cikin al’ummar Maro a masarautar Kufana, dake  karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suka sace Hakimin kauyen, Mista Obadiah Iguda.

Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar, 28 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 1:00 na dare, lokacin maharan na dauke da muggan makamai suka dira kauyen, suka kutsa har cikin gidan hakimin suka yi awon gaba da shi.

Advertisement

Kwankwaso ya ci amanarmu, Mun bar wa APC shi – NNPP

Rahoton da shugaban kula da yankin Kufana, Mista Stephen Maikori, ya aike wa Mai Martaba Agom Kufana, ya bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da hakimin ne kawai, ba tare da kashe ko jikkata wani ba, kuma ba su kwashe wani abu daga cikin kauyen ba.

> “Wannan mummunan aiki ya kara dagula lamarin tsaro a yankin, kuma yana barazana ga zaman lafiyar al’umma baki daya,” inji Maikori a cikin wasikar da ya aike wa Mai Martaba.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa sace hakimin ya jefa tsarin shugabancin gargajiya na yankin cikin rudani, tare da barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankunan da ke makwabtaka.

Hukumomin masarautar Kufana sun roki hukumomin tsaro da su gaggauta daukar matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Advertisement

Da DAILY TRUST ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce har yanzu suna tattara bayanai game da lamarin, kafin su fito da cikakken bayani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da sace hakimin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending