News
Gwamnatin Kano Ta Yi Alkawarin Samar Da Kayan Aiki Na Zamani Ga jami’an yada labarai Na Kananan Hukumomi
Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga jami’an yada labarai na kananan hukumomi 44 na jihar da su ci gaba da aiki da himma wajen wayar da kan al’umma, musamman kan batutuwan da suka shafi inganta kiwon lafiya da cin abinci mai gina jiki.
Waiya ya bayyana haka ne a lokacin da yake bude taron bita na yini biyu da aka shirya domin jami’an yada labarai, inda ya jaddada muhimmancin yada labarai masu inganci don magance matsalolin lafiya da ke haifar da mace-mace a jihar.
H-S Biggy Foundation Ta Ba Da Tallafin Kuɗi Ga Yara 100 Masu Fama Da Cututtuka A Asibitin Kano
Ya ce, “Babu shakka, za mu ci gaba da ba ku dukkan tallafin da kuke bukata don ku ci gaba da aiki cikin kwarewa. Yana da muhimmanci ku yi amfani da ilimin da kuka samu wajen wayar da kan al’umma kan cin abinci mai gina jiki da kuma kula da lafiya.”
Kwamishinan ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za a samar wa jami’an kayan aiki na zamani don inganta ayyukansu. Bugu da ƙari, ya ƙaddamar da gasa tsakanin su, inda wadanda suka fi fice a aikin za a ba su kyaututtuka a kowane wata.
Mahalarta taron sun yi godiya ga kwamishinan kan shirin bitar, inda suka ce sun samu ilimi mai amfani kuma za su himmatu wajen aiwatar da abin da suka koya.
Taron ya ƙare da alkawarin ƙara haɗin kai tsakanin ma’aikatar yada labarai da jami’an kananan hukumomi domin inganta wayar da kan jama’a kan batutuwan da suka shafi lafiya da ci gaban al’umma.
