News
Gwamnatin Kano Ta Bukaci Jama’a Su Kare Kansu Daga Ƴan Daba Da Masu Kwacen Waya
Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci al’umma da su kasance cikin shiri da himma wajen kare kansu daga hare-haren ƴan daba da masu kwacen waya da ke ci gaba da addabar wasu sassan jihar.
Kwamishinan Tsaro na Jihar Kano, Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi, kamar yadda Premier Radio Kano ta ruwaito.
Kamfanin Facebook Zai Goge Tsofaffin Bidiyoyi Live, Sakamakon Sauye-Sauye A Shafin
Kwamishinan ya bayyana damuwarsa kan yadda ake kara samun yawaitar aikata laifukan daba da kwacen waya a wasu yankunan birnin Kano, yana mai jan hankalin al’umma da kada su zura ido ko su kasance cikin fargaba har su kasa kare kansu.
Ya ce, “Bai kamata mutane su tsaya suna kallon ‘yan daba suna gallaza musu ba, saboda babu wani dalili da zai sa a kasa ɗaukar matakin kare kai. Ba wai saboda sun fi karfin al’umma bane.”
Yace yanzu ba lokaci bane da matasa da ‘yan bijilanti za su rika jin tsoro ko gujewa ‘yan daba da masu kwacen waya ba, yana mai cewa dole matasa su tashi tsaye su kare kansu da iyalansu daga wannan barazana ta kwacen waya da aikin daba.
Kwamishinan ya kara da cewa kamata yayi kowa ya bayar da tasa gudunmawa wajen magance matsalar, ba wai a tsaya ana zagin gwamna a kafafen sada zumunta ba, inda ya ce lokaci ne da za a fuskanci ‘yan daba da takamaiman mataki in har sun kawo farmaki.
AVM Umaru ya bayyana cewa gwamnatin Kano na ci gaba da ɗaukar matakan tsaro tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin dakile ayyukan bata-gari a fadin jihar.
Haka zalika, ya bukaci al’umma da su rika bayar da bayanai ga hukumomin tsaro kan duk wani motsin da suka ga yana iya zama barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu.
Kwamishinan ya kuma ja kunnen matasa da su guji shiga harkokin fadan daba da kuma masu kwacen waya, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani matashi da aka kama da hannu a cikin aikata laifi ba.
