News
Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Jita-jitar Saka Dokar Hana Fita A Wasu Yankunan Birnin
Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an saka dokar hana fita a yankin Kakuri da wasu unguwanni da ke kewaye da shi a karamar hukumar Kaduna South.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr. James Kanyip ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, yana mai bayyana cewa labaran da ke yawo ba su da tushe balle makama.
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Naira Biliyan 2.6 A Jigawa
“Wuraren da ake ta yadawa a cikin wannan jita-jita kamar Kakuri Bus Stop, Kurmi Gwari, Monday Market, Afaka Road, Air Force Junction da Kakuri GRA, dukkansu suna cikin natsuwa, harkokin kasuwanci na tafiya yadda ya kamata kuma babu wata matsala ta tsaro,” inji shi.
Dr. Kanyip ya ce jami’an tsaro suna nan a bakin aiki a wadannan yankuna, inda suke tabbatar da doka da oda tare da kare lafiyar jama’a.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ba ta kafa wata dokar hana fita a Kakuri ko wani yanki na Kaduna South ba, kamar yadda wasu ke yadawa.
Kwamishinan ya gargadi jama’a da su daina yada bayanai marasa tushe da za su iya jefa jama’a cikin firgici da tayar da hankali, musamman a kafafen sada zumunta.
“Mutane su yi watsi da wadannan jita-jita, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali,” inji Dr. Kanyip.
