Connect with us

News

Rikici Na Kara Kamari A Majalisar Tarayya Kan Mulkin Shugaba Tinubu

Published

on

FB IMG 1752352820809

Shugabancin Majalisar Tarayya na fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen majalisa, sakamakon gazawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na biyan dubban ‘yan kwangila da suka kammala ayyukan gwamnati tun shekarar 2024.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da neman sabbin basussuka da darajarsu ta haura Naira tiriliyan, wai don aiwatar da muhimman ayyuka a fannonin gine-gine, noma, kiwon lafiya, ilimi, ruwa, tsaro da samar da ayyukan yi.

Gwamnatin Kano Ta Za Ta Kashe Fiye Da Naira Biliyan 69 Don Manyan Ayyuka

Sai dai masana da ‘yan kasa da dama na caccakar gwamnati, suna masu cewa ba daidai ba ne a rika neman bashin kudade, alhali ana gaza biyan masu hakkin da suka yi wa gwamnati aiki tun watanni tara da suka wuce.

A watan Yuni 2025, sama da ‘yan kwangila 5,000 karkashin kungiyar “Concerned Contractors Owed by the Federal Government of Nigeria – 2024 Capital Projects” suka fitar da bayani, suna rokon Shugaba Tinubu da Majalisar Tarayya da su sa hannu wajen tabbatar da biyan ayyukan da suka kammala tun tuni.

Wata Majiya A Majalisa Ta Fallasa

Wani dan majalisa daga zauren wakilai, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa POLITICS DIGEST cewa shugabannin majalisa na fifita wasu wakilai wajen biyan ayyukan mazaba, musamman masu kusanci da su.

Advertisement

“Idan kana kusa da shugabanni, za a biya maka aikin mazaba cikin lokaci, amma sai ka bayar da wani kaso. Idan kuma baka kusa da su ba, sai a ce kudin bai fito ba. To daga ina ake samun kudin da ake biya wa wasu?” in ji dan majalisar.

Ya kuma yi kashedin cewa rashin biyan kudaden yana janyo matsin lamba daga mazabunsu, inda ake zargin su da karkatar da ayyuka, alhali kuwa su ma ba su samu komai ba.

 

“Idan aka ci gaba da kin biyan wadannan kwangiloli, rikici zai tashi kan  Shugabanni sun  ya gaza.”

MASU KWANGILA NA FAMA DA TALAUCI DA BASHIN BANKI

‘Yan kwangila da dama sun koka da cewa sun karbo rance daga bankuna don kammala ayyukan gwamnati, amma har yau gwamnati ta ki biyan su, lamarin da ke jefa su cikin halin kakanikayi.

“Ba kudi kawai muke nema ba, muna bukatar adalci. Mun yi aikin gwamnati da amana, amma yau mu ake barin cikin bashi, su kuma ‘yan siyasa na wasa da rayuwarmu,” in ji wani daga cikin masu kwangila.

Advertisement

Masana sun bayyana cewa a zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, duk da ana da tallafin mai, gwamnati tana biyan ‘yan kwangila. Amma yanzu da aka cire tallafin mai, wanda aka ce zai samar da karin kudaden shiga, sai gashi har yanzu ana kin biyan wadanda suka yi aiki.

Wannan yana kara tayar da kura kan yadda gwamnatin ke tafiyar da kudin jama’a da kuma gaskiyar manufar cire tallafin.

FARGABAR RIKICIN SIYASA MAI ZAFI

Masana da masu fashin baki sun bayyana fargabar cewa matsalar na iya rikidewa zuwa rikicin siyasa mai tsanani a tsakanin ‘yan majalisar da ma cikin jam’iyyar APC mai mulki.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan majalisa na shirin bijire wa shugabannin majalisar bisa zargin yin son kai da rike kudi.

Idan aka gaza warware wannan matsala, ana fargabar cewa gwamnatin Tinubu za ta kara fuskantar rashin amincewa daga al’umma da kuma daga wakilan da ke wakiltar su a majalisa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending